Boko Haram: Daya daga cikin yan ta'ada da suka saci yan matan Chibok zai yi shekara 15 a gidan wakafi

Boko Haram: Daya daga cikin yan ta'ada da suka saci yan matan Chibok zai yi shekara 15 a gidan wakafi

Wasu daga cikin ya matan chibok da aka kubitar daga hannun boko haram

Yahaya wanda a halin yanzu gurgu ne ya nemi kotu ta wanke shi daga zargin da ake masa. Daga baya ya nemi rangwami domin ya aikata hakan ne ba don son ran shi ba.

Babban kotun tarrayya dake garin Kainji na jihar Niger ta yanke ma daya daga cikin yan ta'addar boko haram hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekaru 15.

Mai laifin Haruna Yahaya mai shekara 35 a duniya ya samu hukuncin a zaman da kotun tayi ranar litinin 12 ga watan febreru 2018 bayan an kama shi da laifin sa hannun wajen sace yan matan chibok cikin 2014.

Yahaya wanda a halin yanzu gurgu ne ya nemi kotu ta wanke shi daga zargin da ake masa. Daga baya ya nemi rangwami domin ya aikata hakan ne ba don son ran shi ba.

Labari yazo mana cewa wannan tsohon dan ta'addar yana daya daga cikin yan boko haram da suka kai hari garin Chibok dake karamar hukumar Chibok da kuma garin Gabsuri dake karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

Mai sharia kan karar da aka shigar yace ba za'ayi la'akari da labarin da ya fitar tare da tausaya masa bisa nakasun da yake fama da ita.

Mai sha'riar ya zarce hukunci na fara zaman shi a gidan yari daga 12 ga wata duk da cewa shi dai Yahaya yana hannun jami'an tsaro tun 2015.

*Shakau ya saki sabon bidiyo, yace a shirye suke domin yakar jami'an tsaro(Bidiyo)

Yan matan chibok

A daren ranar 14 ga watan afrilu na 2014 kungiyar Boko Haram ta far ma al'ummar garin Chibok inda har suka samu nasarar sace yan makaranta mata su 276.

Bayan yan watannin da faruwar hakan mata 57 sun samu damar tsere wa daga sansanin yan ta'adar.

A cikin watan Mayu na 2016 daya daga cikin matan mai suna Amina Ali ta sanar cewa har ga lokacin sauran matan suna nan garkame a sansanin yan ta'addar amma 6 daga cikin su sun rasa rayukar su. Ta sanar da hakan bayan ta samu nasarar kubuta daga hannun boko haram sanadiyar harin da jami'an tsaro suka kai masu.

Cikin watan oktoba na 2016 kungiyar ta saki mata 21 na daga  cikin yan matan bayan haka a watan mayu na 2017 ta kara sakin 82 kan wata yarjejeniyar musayya da ta kulla da gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta bukaci a saki kwamandojin ta da jami'an tsaro suka kama.

2,121
Like
Save

Comments

Write a comment

*